ZABEN EKITI: Secondus ya jagoranci zanga-zanga zuwa Majalisar Tarayya

0

Wasu mambobin jam’iyyar APC sun dira Majalisar Tarayya domin zanga-zangar nuna yin tir da abin da ‘yan sanda suka yi wa magoya bayan jam’iyyar ta su a Ekiti.

Shugaban jam’iyyar Uche Secondus ne da kan sa ya jagoranci zanga-zangar.

Sai dai kuma jami’an tsaro ba su bar su sun shiga cikin harabar majalisar ba.

A inda suka tsaya bakin kofar shiga, Secondus ya ce sun je ne domin su mika takardar kukan su ga majalisa cewa ba su yarda da abin da aka yi wa magoya bayan su jiya Laraba a Ekiti ba.

Secondus ya ce abin da ‘yan sanda suka yi wa Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, ba shi da bambanci da juyin mulkin a zamanin mulkin siyasa.

Ya ce duniya ta cika da mamakin yadda aka wulakanta gwamnan PDP da magoya bayan sa ana kwana uku kafin zabe.

Secondus ya ce an hana al’ummar Ekiti fitowa su yi walwala a jajibirin ranar zabe, saboda an mamaye jihar da jami’an tsaron gwamnati mai mulki da ke son tilas sai ta kwace jihar daga PDP.

Daga nan sai yace wannan ya na nufin gwamnatin tarayya za ta yi a-ci-ko-da-tsiya kenan a zaben na ranar Asabar mai zuwa.

PDP Protest at Senate

PDP Protest at Senate

Ya kara kokawa a kan yadda aka tsorata magoya bayan su kuma aka firgita su tare da kashe musu guiwa ta hanyar yin amfani da ‘yan sanda da nufin sai an ci zabe da tsiya.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ne ya tarbe shi tare da karbar wasikar koken na su.

Mataimakin ya ce ya saurari koken kuma zai kai shi gaba domin a dauki kwakwaran mataki.

Uche ya ce dimkokradiyya ‘yanci ce, matsawar ba a bin doka da bayar da ‘yanci, to wannan dimokradiyya da sauran rina a kaba kenan.

Share.

game da Author