Jam’iyyar PDP da APC duk an same su da rarrabawa masu zabe kudade.
A wani bidiyo da wakilin mu ya dauko ya nuna wani wakilin jam’iyyar APC mai suna Bello Dauda na rabawa wasu mata kudi su zabe jam’iyyar sai dai kma jim kadan bayan mun fallasa wannan abin kunya sai wani dan PDP Adetunji Ojo ya bayyana cewa hakan ba jam’iyyar APC kawai bane suka yi haka.
” Wannan abu har da mu ‘yan PDP muka yi ta raba wannan kudi sai dai mu ba mu bada da yawa ba. PDP sun bada kasa da naira 5000 ne. Amm dai babu komai duk da rasa wannan mazaba ta mu da muka yi.
An dai tabbatar da cewa a wurare da yawa cewa jam’iyyar da tafi raba kudi ne aka fi zaba.
Discussion about this post