Za mu kawo muku cikaken rahoton abin da zai wakana daga farko har karshe tare da hotuna da bidiyo dalla-dalla.



EKITI 2018: An samu rahotannin fizgen akwatunan zabe
PREMIUM TIMES ta tabbatar da samun rahotannin fizgen akwatinan zabe a wasu daidaikun mazabu a jihar Ekiti.
Daya daga cikin wurin da aka fizgi akwatin dai, an yi nasarar guduwa da shi, ba tare da jami’an tsaro sun kama kowa ba.
Yayin da a daya wurin kuma jami’an tsaro sun ci galabar hana ‘yan daba arcewa da akwatin.
Wani da har yau ba a gano ko wane ne ba, ya dauki akwati a rumfar zabe mai lamba 12, ta mazaba ta 6 a Karamar Hukumar Efon Alaye.
Ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a gaban idon jama’a barawon akwatin ya fizge shi ya tsere.
Hakan ya sa wasu da dama tserewa zuwa gida, gudun abin da ka iya biyowa daga baya.
Zauna-gari-banzan dai sun dira mazabar da misalign karfec 12:17 na rana.
Dattawa maza da mata sun fito zabe
Wakilan PREMIUM TIMES da ke Ekiti sun bada rahoton cewa dattawa maza da mata sun nfito sosai wajen kada kuri’ar zaben gwamnan jihar Ekiti
Wakilan mu sun ga dattawa a mazabun makarantar St.Anne da ke Isasa da Usi ta Karamar Hukumar Ido/Osi.
Da yawan su kuma sun fito domin kada kuri’a a mazabar Emure da Amaroko.
Ejan ya yi barazanar guntule hannun wanda ya zabi PDP
Zabe ya tsaya cak na wani lokaci, a lokacin da wani ejan ya yi barazanar guntule hannun wanda duk ya zabi PDP.
Abin ya faru ne a lokacin da wani uban rigimar ejan ya dira a mazabar Igbemo ta cikin Karamar Hukumar Irepodun-Ifelodun.
Mutumin mai suna Kazeem ya dira wurin da misalin karfe 9 na ranar yau Asabar a lokacin an fara kada kuri’a.
Ya na isa sai ya fara hargowa a cikin harshen Yarbanci, ya na cewa kowa ya zabi APC, wato Kayode Fayeme.
“Ku zabi APC. Duk wanda ya zabi PDP za a datse masa ‘yan yatsun hannu.” Haka Kazeem ya rika fada ya na ta nanatawa, amma da sharshen Yarbanci.
Wannan furuci ya janyo masa sa-in-sa shi da wani mai goyon bayan APC da ake kira Ojo, wanda ke kan layin jefa kuri’a.
Ojo ya fusata, inda ya fito ya tunkari Kazeem kaib tsaye.
PDP ta doke APC a mazabar gwamna Fayose, Afao, Irepodun-Ifelodun
AD – 1
ADP – 1
PDC – 1
Pandel — 1
APC – 106
PDP — 304
Void — 29
RAC 1 PU 6 ward 10 gbonyin LGA… Result announced as at 2:30pm
PDP — 94
APC — 72
APDA — 1
YPD — 1
Void — 10
Ward 9, Unit 3, Efon Alaye LGA.
AA 1, APA 1,APC 36, PDP 65,
ODO ISE II, presiding officer – MGBECHI JOY UJUNWA
AD- 2
ADP- 1
APA- 1
APC- 144
PDP- 68
PPA- I
A Ward 9, Unit 5, RAC centre, Efon High school, Efon Alaye LGA APC 23, PDP 52, AD 1,
APC na hanyar yi wa PDP zigidir a zaben Ekiti
Alamu dai suna nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki a kasa na hanyar yi wa jam’iyyar PDP a Ekiti zigidir bisa ga sakamakon zaben da suka faro samuwa zuwa yanzu.
A kusan duka mazabun da suka manna amintacciyar sakamakon zabe da muga samu kuma muka gani kai tsaye ya nuna cewa APC ne ke samun mafi yawan kuri’u.
Sai dai kuma PDP ma ta gwabza wa da APC din a wasu mazabun.
Ku bimu a nan kai tsaye domin samun sakamakon zaben daga duk mazabun jihar Ekiti daga wakilan mu.





PDP ta budo wuta, ta ce ta na bibiyar sakamakon zaben daki-daki
Jam’iyyar PDP ta gargadi hukumar zabe da kada ta kuskura ta murde mata zabe domin kuwa tana bibiyan abinta sau da kafa.
Yanzu fa zaben ya na canza launi domi PDP ta bude wuta.
Ikole West 1, Polling Unit 002 at Holy Apostolic Pry School. ACD: 1. ADP: 1. APA: 2. APC: 107. PDC: 5. PDP: 169.
Ikole West 1, Polling Unit 003 at Chief Oye’s House. APA: 2. APC: 96. NPC: 1. PDC: 2. PDP: 107. SDP: 1.
Ikole West 1, Polling Unit 1. Accord: 2. APDA: 1. PPA: 1. NPN: 1. PDC: 2. ADP: 1.