Wani masanin kimiyya mai suna Augustine Ubachukwu, ya bayyana cewa a yau Juma’a da dare, za ayi khusufin wata na tsawon sama da awa daya.
Ubachukwu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, wannan bayani na khusufin wata, a yau Juma’a da dare.
“Za a yi khusufin wata daga tsakanin 9:30 zuwa 11:22 na dare, kuma za a fuskancin wannan yanayi ne tun daga daukacin shiyyar duniya ta gabas gaba daya, da ta hada da Turai, Afrika, Asia, Australiya da New Zealand.
Ya kara da cewa wasu kasashen da ke nahiyar Amurka ta Kudu ma za su fuskanci khusufin amma a lokacin da ya ke kusa da karewa.
‘‘Wannan mafi tsawon khusufin wata da za fuskanta. Zai dan fara disashewa ne tun daga 7:24 na dare, sai ya disashe gaba daya can wajen 8:30 na dare, daga nan zai yi duhu dundurun daga 9:22 na dare har zuwa 11:19 na dare, inda daga nan kuma sai ya fara wasashewa haske na kara bayyana daga 11:22 na dare.’’ Inji Ubachukwu a bayanin sa jiya Alhamis a Abuja.