Shekara daya bayan da kamfanin yin kayan masarufi da amfanin gida mai suna Procter and Gamble, ya gina katafariyar masana’antar yin kunzugun mata masu jinin al’ada da na jarirai, wato ‘Always’ da ‘pampers’, tuni har an kammala batun rufe masana’antar bayan da aka kashe kimanin dala miliyan 300 wajen kafa ta.
Wannan katafaren kamfani dai ya na a sahun gaban samar da kayayyaki, kuma an kafa masana’antar ce a garin Agbara cikin Jihar Ogun.
PREMIUM TIMES ta samu tabbacin cewa kamfanin ya yi tunanin kafa babban reshe a nan Najeriya ne cikin 2017, ta hanyar gina wannan masana’anta da aka ce an kashe mata dala miliyan 300.
An kafa masana’antar ce da niyyar rika sarrafa kunzugun mata da na jarirai da omon wanke-wanke.
Kwakkwarar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa a zaman yanzu an sallami ma’aikata 120, wadanda tuni suka karbi takardar sallama, kowa zai kama gaban sa nan da karshen wannan wata na Yuli.
“An ce za a dan bar ma’aikatan da ba su wuce 30 ba, suma domin wasu ayyaukan da ba a tantance ba.
Wannan kamfani shi ne ke sarrafa kayan da suka hada da ‘Always’, ‘diapers, sabulun Ariel, Oral B, rezar aski Gillete, da sauran su.
Za a rufe kamfanin shekara daya kacal bayan da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbjo da gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun suka kaddamar da bude shi
BA WANNAN NE FARAU BA
Kafin Procter and Gamble ya fara shirin rufe masana’antar kunzugu ta Agbara, ya fara sayar da wata masana’antar a Ibadan, cikin Jihar Oyo. Shi ne ake yin alawar tsotso ta lemon vicks da omo Ariel.
” Dole mu saida wannan kamfani namu dake Oyo, domin in banda hasara babu ribar da muke samu da wannan kamfani.”
” Dayan kamfanin da ke garin Ibadan ma ya na kan gaba, saidai zamu dan jira mu gani ko za mu iya ci gaba da aiki tukunna.
TAKAICI GOMA DA ASHIRIN
An gina wannan kamfani a lokacin da gwamnatin Buhari da sauran ‘yan Najeriya ke murna ganin cewa dimbin matasa za su samu aiki, amma abin takaici sai ga shi cikin shekara daya da kafa shi ana shirin rufe ta.
Bincike ya nuna cewa a cikin 2016 an rufe manyan masana’antu har 276 a cikin kasar nan.
Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa babu yadda za a yi masana’anta ta dawwama ko ta samu gindin zama a Najeriya, ganin yadda har yanzu dala daya ta na daidai da naira 365.
Wani babban dalilin kuma shi ne masana’antun ba su da wata kariyar samun jari daga hannun gwamnati idan suka durkushe.
Discussion about this post