Za a Iya Gane Kishin ‘Yan Najeriya A Zaben 2019, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Alhamdulillah,siyasa ta fara daukar zafi a kasar Najeriya tsakanin talakawa da masu neman mulki.

In Allah yaso siyasar kasarmu ta dauko hanyar gyaruwa duba da yadda adawar siyasa ta samu gindin zama. APC ce jam’iya mai mulki amma tana cikin matsanaicin matsin lamba daga ‘ya’yanta da suke mata barazanar barinta su kafa jam’iyar rAPC da kuma jam’iyar adawa ta PDP da ta sha kayi a wajenta a zaben 2015.Hakan ya zaburar da ita kai tsaye wajen tabbatar da yin “hannun kar6a,hannun mayarwa”.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Ga kuma barazanar da sabuwar PDP takeyi itama a gefe daga bangaren tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Adawar siyasa tana kawo cigaba, don rashin ‘opposition’ wato ‘yan adawa a siyasa baya nuna ci gaban ta. Mulkin Najeriya akwai dadi shiyasa ba kowa bane yake sauka daga shi ya samu kwanciyar hankali.Nazari ya nuna cewa babu sana’ar da ta kai siyasa riba a kasarmu shiyasa mutane da yawa sun fito neman kujerar mulkin kasar saidai Allah ya taimaki talakawa da makamin qare dangi a filin zabe.

Ita ce kuri’a idan sun yi amfani da katin zabensu ta hanya mai kyau.Babu wanda bai rike mukami ba an ga kamun ludayinsa a cikin manyan ‘yan siyasar da suke ta neman hadin kan talaka a yanzu saboda haka ya ragewa talakawan su aunasu da ma’auni na ilimi don Najeriya ta ci gaba.

Ban ce maka ka zabi Buhari ba ko kada ka zabe shi, amma kamar yadda ya fada idan kana da wanda ya fishi ka zabe shi kai tsaye. Wannan dama ce ga masu son ci gaban kan su. An dade ana shan wahala a Najeriya, kuma a cikin masu neman mulkin kasar a yanzu akwai da yawa daga cikinsu a cikin gwamnatin baya.

Abun tambaya a nan shine, me suka samawa talakawan Najeriya kafin damar ta kubuce musu? Ko yanzu ne suka hango gyaran suke shirin yi? Ko kuma lalitarsu ce take shan mazga daga buqatunsu na yau da kullum shine suke neman sake cikata da dukiyar talaka? Sannan ita gwaunatin da take kai me takeyi don kaucewa abunda ya faru a baya.Wannan hisabin yakamata ka yi kafin ka dangwala babban yatsanka akan kuri’ar za6e.Idan kuma siyasar kudi kafi so,to ga fili ga mai doki nan.Kai da wahala kun auri juna.

Najeriya ta dade a cikin siyasar kudi, amma ni dai bansan mutum daya da yaci ribarta ba ban kuma ce babu ba. Mafi munin abun shine su baku kudin ku kashe daga baya kuma Ku dawo talaucinku.Tun 2003 wasu suka mayar da siyasar kudi Sana’a, suke debo mata da maza masu mutuwar zuciya ana basu kudi kadan suna za6ar mutumin da basu Sani ba a mu’amilance.

Wallahi da yawansu sunfi kowa shan wahalar Najeriya saboda sun zama “su basu dauko ba,su ba’a daukosu ba” Allah ya rabamu da abunda ba riba kuma ba lada.Muna bayar da shawara ga talakawa wadanda jikinsu yake gaya musu a mulkin kasarsu da su saka nutsuwa don Najeriya ta gyaru da ikon Allah.Kuzo mu yi iya yinmu,kammala ta Allah ce,idan yaso sai kasar ta gyaru.

Allah ya gyara mana.

Share.

game da Author