Wani likita mai suna Okezie Emenike ya bayyana cewa rama da kiba a jiki ga namiji ko mace na iya hana samun haihuwa.
Ya fadi haka ne don wayar da kan mutane musamman wadanda ke fama da rashin haihuwa hanyoyin da za su bi domin kubuta daga matsalar da suke fama da ita.
Emenike ya bayyana cewa hakan na yiwuwa ne sanadiyyar rashin iya sarrafa sinadarorin da ke taimakawa wurin samun ‘ya’ya a jikin mace ko namijin dake fama da kiba ko kuma rama.
Likitan ya ce mutanen da suke fama da wannan matsala za su iya kubuta ne idan suna cin kayayyakin lambu, ganyayyakin dake kara lafiya, motsa jiki tare da samun hutu.