Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta damke wasu ‘yan Boko Haram takwas tare da wasu masu hada baki da su, da suka ce su na da hannu wajen sace daliban Chibok a cikin 2014.
An kuma bayyana wasu da ake zargi daukar nauyin kai wasu hare-haren kunar bakin wake da kananan ‘yan mata suka rika kaiwa. Wadannan kuma su 14 ne.
An bayyana wannan kamun ne yayin wani taron manema labarai da hukumar ‘yan sandan ta yi yau Laraba a Maiduguri, babban birnin jihar.
Akwai Mayinta Modu da ake kira Abor mai shekaru 20, Adam Mohammed, 20; Gujja Jidda, 21,Mamman Wardi, 25, Modu Jidda, 29; Ajiri Bulama Dungus, 22; Mohammed Abba, 20; Fannami Mustapha,
Abdullahi Mohammed Gawi, 23; Maina Adam, 35; Wano Musa, 27; Ishaka Musa, 26; Abubakar Mohammed, 28; Usman Umar, 28; Maina Abba, 27; Maina Gambo, 24; Abubakar Kori, 25; Bukar Abatcha, 39, Ibrarahim Mala, 48 da Mustapha Kanimbu, aka Aaramma.
An sace daliban Chibok 270 a cikin 2014.
Daga a farkon 2017, an tattauna da Boko Haram suka sako 100 daga cikin su.
Discussion about this post