Jami’an ‘yan sanda sun cafke dan takarar gwamna mai suna Grema Terrab, a wurin taron siyasar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a Maiduguri.
Da dai jami’an SARS sun buga sanarwar neman sa ruwa a jallo tun kafin wannan ranar.
‘yan sanda na neman sa ne a bisa abin da suka kira zargin rasa ran da wata mata ta yi a gidan sa yayin da ake wani taron siyasa a cikin watan Afrilu.
Duk kuwa da cewa Terrab din ne ya kai rahoton mutuwar a ofishin ‘yan sanda, sai suka cafke wasu daga cikin iyalan sa, ciki kuwa har da matar sa Saadatu Mohammed, wadda a lokacin sai da PREMIUM TIMES ta buga labarin kamun na ta da aka yi.
An tsare ta tsawon makonni, har ta yi bari a hannun ‘yan sanda, saboda an tsare ta ne a lokacin ta na da ciki.
Sai bayan da ta yi bari ne aka bada belin ta.
A wannan ne karon farko da Terrab ya bayyana a Maiduguri tun wancan lokacin da aka daina ganin sa.
A halin yanzu dai akwai fostar sa ta neman takarar gwamna da kuma alluna an kakkafa ko’ina a cikin Maiduguri.
Jami’an SARS sun ji labarin Terrab ya shigo gari wurin taron Atiku, sai suka yi wa wurin tsinke, suka yi cincirindo, ciki kuwa har da wasu a cikin kayan gida.
Wakilin PREMIUM TIMES ya ga yadda wasu hadiman Terrab suka rika rokon SARS kada su kama shi.
Sai da suka bari Atiku ya kammala jawabi ya zo ficewa, sai suka wuf suka rike Terrab ta baya, wanda a lokacin ya na kusa da Atiku.
Terrab ya yi kokarin nusas da Atiku halin da ake ciki, ta hanyar janyo masa riga ta baya, amma sai jami’an tsaro suka tare, sannan su kuma SARS suka yi gaba da Terrab suka saka shi mota, suka fice.
Jami’an tsaron sun hana masu daukar hoto su dauki yadda aka yi tataburzar ficewa da Terrab.
Har zuwa yanzu dai ‘yan sanda ba su itar da wani jawabi dangane da kamun da suka yi wa dan takarar gwamnan ba.
Discussion about this post