Tsare-tsaren gwamnatin Buhari zai rika samar da ayyuka miliyan 3.7 duk shekara – Minista

0

Ministan Harkokin Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Okechukwu Enelamah, ya bayyana cewa Shirin Farfado da Tattalin Arzikin Kasa da aka shigo da shi, zai rika samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya miliyan 3.7 a kowace shekara.

Ya ce wadannan ayyukan za su samar da zuba jari a kayayyakin more rayuwa da masana’antu, wanda hakan zai kara samar da ayyukan yi ga al’umma.

Ministan ya kara cewa an fi maida hankali wajen samar da aikin ne ga matasa domin tabbatar da cewa su din ne suka ci moriyar wannan tsari.

Ya ce daga nan zuwa 2020 ana sa ran samar da ayyuka ga matasa har miliyan 15.

An dai gudanar da wannan taro ne ne a Abuja, ta hadin kai da wata kungiyar da ke kasar Amurka tare da hadin gwiwa da Gidauniyar Citi Foundation.

A cikin watan Afrilu, 2017 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a bisa kudirin nan da 2020 zai samar da ingantaccen tattalin arzikin kasa a Najeriya.

Share.

game da Author