TAMBAYA: Wane Abu ne Allah ya fi so daga wajen bawan sa ya yi masa?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW. Allah ta’ala yana kishi, kuma kishinsa ga bawansa she ne ya aikata abinda ya haramta. Kuma Allah yana son bawansa ya aikata abun alhairi kumai kankantar sa.
Amma aiyukan alhairi ba suda kankanta, matukar bawa ya dace da karbawar Ubangijin sa.
Aiyukan da Allah ya fi so daga wajen bawan sa ya aikata sunada yawa, don sun bambanta daga wuri zuwa wuri, zamani zuwa wani zamanin, lokaci zuwa lokaci, halin rayuwa na yau da gobe da kuma bambancin mutane da bukatun al’uma. Misali karatun Alkur’ani da sallolin nafila sunada girma a cikin Ramadana ako ina a duniya, amma kuma idan a ka yisu acikin Harami ko Masallacin Annabi sunada wani kwarjini na musamman.
ABUBUWAN DA ALLAH YA FI SO DAGA WAJEN BAWAN SA
1) Aikata duk abinda aka farlanta a kan lokaci cikin ilimi da Ikhalasi ga Allah.
2) Sallah cikin lokacinta, itace rukuni na biyu kuma ginshikin addina, tana tsarkake bawa daga zunubbai kuma itace farkon abinda za’a yiwa bawa hisabi.
3) Jihadi don daukaka addinin Allah, yaki don kawar da shirka, zalunci, kafirci, kira zuwa ga Kalmar Allah ta kowace hanya.
4) Amfanar da mutane da farantawa al’umma rai, ta kowace irin hanaya, kamar Murmushi da shimfidan fuska, biyan bukaka, ya ye bakin ciki, ciyarwa tufatarwa…
5) Dawwama akan aikin alhairi. Wato lazimtar wani aiki ba tare da yankewa ba.
6) Sassauci da tsakaici a cikin al’amarin addini da da rayuwa.
7) Biyayya ga iyaye.
8) Hakikanin imani da yakini ga Allah.
9) Sadar da zumunta.
10) Umurni da kyakkyawa da hani da mummuna.
11) Zikirin Allah ta’ala. Kuma ma fi girma “subhana lillahi wa bi hamdihi”
12) Tsage gaskiya a wajen ja’rin shugaba cikin hikima.
13) Gaskiya a cikin aiki da Magana.
14) Kyakkyawan dabi’a da kyakkyawan hali.
15) Sama ‘ya’ya sunan Abdullahi ko Abdurrahman.
Allah shine mafi sani
Discussion about this post