Saraki da Dogara sun yi Allah-wadai da yunkurin tsige Gwamna Ortom

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, sun yi Allah wadai da tuggun da aka kulla domin tsige Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom daga kan mulki.

Wasu ‘yan majalisar jiya ne su takwas ‘yan APC, daga cikin mambobi 30 suka yi yunkurin a lokacin da ‘yan sanda suka ba su kariyar shiga majalisar su yi zama a yau Litinin.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun hana sauran mambobi 22 ‘yan PDP shiga cikin majalisar.

Daga nan sai ‘yan majalisar na APC su takwas suka aika wa Ortom da takardar sanar da shi zargin da suke yi masa, wanda shi ne suka ce dalilin su na yin yunkurin tsige shi.

Saraki da Dogara sun yi wa Buhari hannun-ka-mai-sanda cewa ya umarci ‘yan sanda su shiga taitayin su wajen yadda aka maida su karnukan farauta, ana amfani da su wajen biyan bukatun siyasa ido-rufe.

Sun ce abin da ya faru a Benuwai haramtacce ne, kuma ba a bitsari ko sharuddan da doka ta gindaya idan za a tura wa gwamna takardar sanarwar tsige shi ba.

Sun kuma yi matukar mamakin yadda aka yi amfani da ‘yan sanda aka rufe ‘yan majalisa takwas a zauren majalisa, aka hana 22 shiga, abin da suka ce dimokradiyya ba za ta taba amincewa da wannan karfa-karfa ba.

“Mu abin da mu ke kallo a nan shi ne, irin cin mutuncin da ake yi majalisa, wanda ya tabbatar da cewa tilas a rika yi wa Najeriya kallon cewa dimokradiyyar kasar ta koma irin zamanin mulkin karfa-karfa, wanda shi ne aka kora aka kafa dimokradiyya.

Saraki da Dogara sun kara da cewa duk wani mai kishin dimokradiyya a ciki da wajen kasar nan, tilas ya fito ya la’anci abin da wasu kalilan suka nemi su yi a jihar Benuwai.

Sun ce wannan shiri ne na karya dimokradiyya a kasar nan, wanda duk mai kishin kasar nan ba zai amince da shi ba.

Sun ce dama can jihar Benuwai ana cikin zaman dar-dar, sai kuma ga shi wasu ‘yan ka-yi-na-yi na kokarin kara jefa jihar cikin rikicin siyasa domin biyan bukatar su.

Daga nan sun yi magana kan haramcin zaman majalisar domin adadin da ya kamata su yi zaman su cika ba, sannan kuma kakakin da aka tsige ne ya jagoranci zaman majalisar.

Da ya ke maida martani dangane da sammamcin da ‘yan majalisar takwas suka aika masa, an ruwaito Ortom a jaridar The Cable da Sahara Reporters ya na cewa shi abain ma dariya ya ba shi.

Daga nan sai ya ce, “sai yanzu ne ma ya fahimci kalamin Shugaban Amurka Donald Trump, da ya ce ‘‘wasu kasashen ba su da bambanci da kofar fitar da bayan gida, domin ba su da wani amfani banda kawai kofa ce ta fitar najasa kawai.”

Share.

game da Author