Duk da cewa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta soke zaben Sanata Atai Aidoko na jihar Kogi ta Gabas, a ranar Talata dai sanatan ya halarci zaman majalisar dattawa.
A ranar 13 Ga watan Yuni ne dai kotun ta tsige shi kuma ta ce kujerar ta sa ta zama fanko, ba kowa a kai har sai an yi wani zabe.
Babban Mai Shari’a Gabriel Kolawole ne ya tsige sanatan dan PDP, bayan da ya tabbatar da rashin ingancin zaben fidda-gwanin da aka gudanar a watan Disamba, 2014.
Kolawole ya ce ba Aidoko ba ne ya cncanci zama dan takarar jam’iyyar PDP ba.
Yayin da PDP ta bayyana nasarar Aidoko, sai abokin karawar sa, Isaac Alfa ya kai kara inda ya nuna rashin cancantar Aido.