SABON RIKICI: An kashe Fulani, an kone musu gidaje sama da 100 a Jihar Adamawa

0

Akwai fargabar cewa an kashe Fulani da dama a wani harin da aka kai musu cikin daren jiya Asabar cikin kauyuka biyar na Fulanin.

Kauyukan da aka kai wa harin sun hada da Bidda, Wubaka, Kaurami Ngengle da Wuro Jauro da ke cikin Kananan Hukumomin Mayo Belwa da Demsa.

Shugaban Karamar Hukumar Mayo Belwa ya tabbatar da faruwar harin da ya ce bai san adadin rayukan da aka kashe ba, amma dai an kona gidaje sama da 100.

Da aka tuntubi Kakakin ‘Yan sandan Adamawa, Othman Abubakar, ya tabbatar da afkuwar kai harin, kuma ya se tuni aka tura ‘yan sanda da sojoji sun garzaya yankunan.

Share.

game da Author