Hukumar Kula da Jami’o’i na kasa, NUC ta amince da wasu sabbin Darussa 37 da ake koyar dasu a jami’ar jihar Kaduna.
Kakakin Jami’ar Adamu Bargo ne ya sanar wa Kamfanin Dillancin Labarai wannan ci gaba da jami’ar ta samu.
Adamu ya ce bayan haka an amince da wasu Darussa hudu a bangaren karatu na gaba da digirin farko wato Mastas da Phd.
Darussan da aka amince da su sun hada da MBBS, B.sc Mathematics, B.sc Microbiology, B.sc Biochemistry, B.sc Biology, B.sc Geography, B.sc Economics, B.sc Political Science,
B.sc Sociology, B.sc Physics, B.sc Chemistry, B.sc Industrial Chemistry, B.sc Estate Management, B.sc Environmental Management, B.sc Architecture da sauran su.