Rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina ta bayyyana mutuwar wsu ‘yan mata hudu sanadiyyar hadarin kwale-kwale a Madatsar Ruwan Mashigi, cikin Karamar Hukumar Kankara.
Kakakin jami’an tsaron Gambo Isah ne ya ce hadarin ya afku ranar Lahadi da rana tsaka.
Ya kara cewa dukkan mamatan ‘yan kauyen Danzango ne, sun shiga kwale-kwalen da niyya a tallaka da su tsallaken dam su sayo kayan masarufi a lokacin da kwale-kwalen ya tuntsire da su.
Isah ya bayyana sunayen mamatan da Yasira Suleiman, Shafawu Saidu, Firdausi Ibrahim da kuma Rakiya Isa, dukkan su ‘yan shekara 16 da haihuwa.
Wasu mutane biyu da aka ceto a cikin ruwan, an garzaya da su asibitin Kankara domin a yi musu kulawar gaggawa.
Ya de Maryam Zubairu mai shekaru 13 da matukin jirgin, Abdullahi Muntari ne suka tsira.