RIKICIN MAKIYAYA: Fadar Shugaban Kasa ta dora laifin kan canjin yanayi da ‘yan siyasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana kashe-kashen da ke faruwa da ake dangantawa da makiyaya da Fulani, ya faru ne sakamakon canjin yanayi.

Fadar kuma ta kara da nanata ikirarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa ‘yan siyasa ne ke kara rura wutar rikicin, kuma ya ce ya na da kwakkwarar shaidar da ke tabbatar da haka.

“Fadar Shugaban Kasa na jan hankalin jama’a da su guji yada jita-jita da kuma labaran karya da kalaman haddasa kiyayya da rikici.”

Haka Garba Shehu ya bayyana. Shehu shi ne Babban mashawarcin Buhari kan yada labarai.

Ya kara jaddada alkawarin shugaba Buhari na kawo karshen kashe-kashen.

Sau da dama Buhari na dora laifin kashe-kashen a kan tsohon shugaban kasar Libya, Mu’amar Gaddafi.

“Gwamnatin Najeriya na aiki kafada-da-kafada da gwamnatin jihohi da sauran hukumomin tsaro da kasashen ketare wajen magance wannan matsala.

“Rikicin makiyaya da manoma ya na da dadadden tarihi sosai.

“Idan muka kalli matsalar canjin yanayi, kamar kafewar tafkin Chadi ya haifar da matsin-lamba kan al’ummar Arewacin Najeriya, wanda hakan ya kara haifar da matsalolin.

Garba ya ci gaba da cewa matsalar canjin yanayi ta shafi duniya da kasashen da ke makwautaka da kasar nan, ba Najeriya kadai ba.

Share.

game da Author