RIKICIN APC: R-APC ta nemi INEC ta haramta shugabancin su Oshiomhole

0

Shugaban sabuwar jam’iyyar R-APC, Buba Galadima, ya rubuta wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), doguwar wasikar da ya nemi ta haramta shugabancin su Adams Oshiomhole.

Wasikar dai na ta dauke da hujjojin da hasalallun ‘yan APC din da suka balle suka kafa sabuwar jam’iyyar suka bayar ga INEC, tare da jera mata sunayen shugabannin kaf baki daya da suka nemi a haramta cancantar su.

Kadan daga cikin dalilan da suka bayar, sun hada kawo hujjojin cewa zaben da aka gudanar na shugabanninn mazabu a ranar 2 Ga Mayu, cike ya ke da danniya, murdiya da rashin adalci.

Haka shi ma zaben shugabanninn jam’iyyar na kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 5 Ga Mayu, an yi shi cikin rikici da tauye wa wasu da dama hakki, har ya haifar da kashe-kashe da kone-kone.

Ba a nan suka tsaya ba, Galadima y ace zaben shugabannin jihohi na 5 Ga Mayu, ya kara haifar da rashinn hadin a cikin jam’iyyar, bugu da kari kuma a wasu jihohin ko zaben ma ba a yi ba.

Galadima ya kara da cea shi ma zaben shugabannin na ranr 23 Yuni, ba a bisa ka’idar da jam’iyya ta shimfida aka gudanar da shi ba.

Ya ce jihohi 22 da suka hada da Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Cross-River, Delta, Enugu, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Niger, Ondo, Oyo, Rivers, Sokoto duk kowa ya shaida irin yadda ta kaya, ciki har da jihar Zamfara.

Galadima ya tunatar wa INEC cewa akwai rahoton da jami’an ta suka rubuta daga kowace jiha, wannan ma ya isa INEC din ta yi amfani da shi wajen yi wa zaben hisabi.

Ya kara da cewa bulkarar da aka gudanar da sunan zabe, ta kauce wa dokar APC ta Sashi na 20(1).

Bayan Galadima ya ci gaba da kara sheka ruwan hujjoji daga cikin kundin dokar kasa da kuma kundin dokar jam’iyyar APC, sai ya lissafa wadanda ya ke so INEC ta haramta mukaman na su na shugabancin APC, da suka hada da:

1. National Chairman – Comrade Adams Oshiomhole.

2. National Welfare Secretary – Alhaji Ibrahim Masari.

3. National Financial Secretary – Alhaji Tunde Bello.

4. National Physically Challenged – by Misbahu L. Didi.

5. Zonal Secretary North-Central – Dr. Zakari Muhammed

6. Zonal Organising Secretary North-Central – Ibrahim M. Abdul.

7. Zonal Women Leader North-Central – Hajia Hassana Abdullahi.

8. Ex-Officio North-Central – Nelson Abba.

9. Zonal Secretary North-East – Abubakar Sadiq Ajia

10. Ex-Officio North-East – Mallam Isah Azare.

11. Zonal Secretary North-West – Tukur A. Gusau.

12. Zonal Organizing Secretary North-West – Abdulmunab Muhammad.

13. Ex-Officio, North-West – Nasiru Haladu Danu.

14. Zonal Woman Leader South-South – Mrs. Rachael Akpabio.

15. Ex-Officio, South-South – Kotenten Ibadan.

16. Zonal Secretary South-West – Ayo Afolabi.

17. Zonal Women Leader South-West – Mrs. Kemi Nelson.

18. Ex-Officio South-West – Omoloye O. Akintola.

Ihun-ka-banza Buba Galadima ke yi, Inji APC

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ihun-ka-banza ne kawai sabuwar jam’iyyar R-APC key i, domin INEC ba za ta iya taimakon su da komai ba. Babban Satakaren APC na Kasa, Bolaji Abdullahi ne ya furta haka a jiya Laraba, yayin da ya ke maida raddin wasikar da ya samu labarin R-APC ta aika wa INEC.

Shugaban sabuwar jam’iyyar, Buba Galadima ne ya sa wa wasikar hannu.

R-APC jam’iyyar wasu hasalallu ne da ke samun goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu dogara, domin su kayar da APC a zaben 2019.

Bolaji ya kara da cewa idan zabe mai yi maka yadda ka ke so ba, kwamitin zabe zaka zai wa kukan ka, ba wai ka garzaya INEC ba. “INEC ba ta iya yi maka komai?

R-APC sojojin rudaddun sojojin haya ne, Inji Oshimhole

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimhole, ya yi watsi da wasikar da Buba Galadima ya aika wa INEC inda ya nemi a rushe shugabancin Oshimhole da kuma sauran shugabannin jam’iyyar,

Da ya ke maida martani jiya, Oshimhole yace wadannan tarkacen da ke kiran kan su R-APC, duk sojojin haya ne.

A cikin bayanin sa, ya ce dukkan wadannan masu barin APC da wadanda suka bari, da masu shirin barin, duk sojan gona ne, dama ba kishin jam’iyya ce a zukatan su ba, sai dai kishin aljifan su kawai

Share.

game da Author