RIGAKAFI: Yara miliyan 123 ne aka yi wa rigakafi a duniya a shekarar 2017- Rahoton WHO da UNICEF

0

Majalisar dinkin duniya (UN) ta bayyana cewa sun sami nasarar yi wa yara miliyan 123 allurar rigakafin cutar tsatasa wato ‘Tetanus’ a duniya cikin shekarar 2017.

Majalisar ta fadi haka ne bisa ga sakamakon rahotannin da WHO da UNICEF suka mika mata.

Majalisar ta ce duk da wannan nasarori da suke samu daga wannan bincike ya nuna cewa akwai yara miliyan 20 a duniya da basu sami yin rigakafi ba.

Bayan haka kuma an gano cewa akwai jarirai sama da miliyan 4 da aka yi musu allurar rigakafi a 2017, da hakan ya nuna an sami kari kan yawan wadanda aka yi wa a 2010.

Rahoton ya nuna cewa kasahe 167 sun hada har da maganin bakon dauro, sannan kuma 162 na amfani da maganin rigakafi na rubella ga jariran da hakan ya sa a ka sami karuwa daga kashi 35 bisa 100 zuwa kashi 52 na wadanda aka yi wa rigakafin.

Wasu daga cikin dalilan da ya sa aka yi ta samun matsaloli wajen yi wa yara allurar rigakafi sun hada da yake-yake da ake fama dasu a kasashen duniya da kuma kuma karyewar tattalin arzikin wasu kasashe musamman masu tasowa da matsanancin talauci.

Bayan haka UN ta ce ta sami maganin rigakafin cututtukan sankara dake kama mahaifa, zazzabin cizon sauro, sankarau da Ebola.

Daga karshe UN ta hori gwamnatoci da su kara yawan kudaden da suke ware wa fannin kiwon lafiya domin samun ci gaba a kasahen duniya.

Share.

game da Author