A gasar cin Kofin Duniya na shekarar 2018, babu wata kasar Afrika da ta taka rawar da ta kai ta ga shiga zagaye na biyu.
Dukkan kasashen da suka wakilci Afrika da suka hada har da Najeriya an koro su gida, tuni har sun manta da sun je wasan cin kofin duniya.
Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne, har yanzu akwai ‘yan wasan da asalin su daga Afrika ne har su 20 da ake ta fafatawa da su, amma su na wakiltar kasashen Turai ne.
Kasar Belgium da ta kori Brazil ta samu hayewa zuwa wasan kusa da na karshe, ta na da ‘yan asalin Afrika da suka hada da: William Carvalho daga Angola, Eder daga Guinea Bissau, Divock Origin daga Kenya, Nasir Chadli daga Morocco, Marouane Fellani daga Morocco, Michy Batshuayi daga Jamhuriyar Kongo shi da Lukaku.
Idan mu ka dubi ‘yan wasan kasar Faransa, akwai ‘yan asalin Afrika har takwas. Dalili kenan idan su na wasa wasu sai su yi tsammani ko wata kasar Afrika ce ke wasa, ba Turawa ba.
A Faransa akwai Samuel Umtiti daga Kamaru, N’Golo Kante daga daga Mali, Kelian Mbappe daga Guinea Bissau da Najeriya, Adil Rani daga Morocco, Blaise Matuidi daga Angola, Steve Mandala daga Jamhuriyar Kongo, sai kuma Ousmane Dembele daga kasar Mali.
Fitattun ‘yan wasan Ingila uku duk ‘yan asalin Afrika ne. Akwai Daniel Alaba shi da Danny Welbeck daga Najeriya sai kuma Leroy Sane dan asalin Senegal.
Akwai wasu ‘yan wasan kuma kamar su Paul Pogba, Dele Ali, da suma suna da asali da nahiyar Afrika.