Gasar cin Kofin Duniya da ke gudana a Rasha, ta zo da ban-mamaki, yadda tun a zagaye na biyu aka kori manyan mashahuran ‘yan kwallon duniya biyu da aka fi ji da su a duniya, Messi da Ronaldo.
Ajantina ta sha kashi a hannun Faransa, ita kuma Portugal ta ci dukan tsiya a hannun Uraguay.
Dama ita Ajantina tun farko da kyar da jibin goshi ta samu fitowa gasar, saboda yadda kwallo ya yi wa Messi santsi.
MESSI: An kara karya alkadarin Messi da Ajantina yayin da Croatia ta ragargaje ta. Messi ya jefa kwallo daya da kyar a gasar, wanda hakan ya kara tabbatar wa jama’a masu sha’awar kwallo a duniya cewa kurin Messi na Barcelona ne, idan ya fita daga kulob din ya zama nama.
A wasan da Ajantina ta ci Najeriya 2-1, kiri-kiri alkalin wasa ya yi wa Najeriya sagegeduwar hana ta bugun daga kai sai mai tsaron gida har sau biyu. Wanda da an yi haka, da Ajantina ba ta samu damar zuwa zagaye na biyu ba.
Wannan ne ya sa awasan jiya Asabar da Faransa ta kori su Messi zuwa gida, ‘Yan Najeriya suke murna da kade-kade, ana yi wa kasar shagube da wakokin muzantawa.
An nuno hoton Messi ya cire riga, nan da nan a wasu gidajen kallon kwallo a Kano, aka rika yi masa sowa ana tafi, ana cewa: “A wanke jersey sai badi.”
A Instagram kuwa, Ajantina da Messi sun sha cakarkaca musamman a hannun ‘yan fim din Hausa abokar zumunci Ahmed Musa, dan kwallon Najeriya.
Hadiza Gabon, Mansura Isa da sauran ‘yan fim da yawa sun rika yi wa Messi shagube. “A gaida gida, Umma ta gaida Aisha.” Haka mawakiya Sadiya Yarima ta rubuta a karkashin hoton Messi.
RONALDO: Duk duniya an yi zaton Ronaldo ya dira gasar nan da kafar dama, ganin yadda a wasan san a farko ya zurara wa Spain kwallaye uku shi kadai.
An kara sara wa Ronaldo a lokacin da ya ci Spain kwallo ta uku da bugun ‘firikik’ ban ban-al’ajabi.
Kafin wannan bugun ‘firikik’, Ronaldo ya buga irin sa a wasannin Portugal sau 44 a jere amma bai yi nasarar jefa kwallo ba, sai a ranar.
Kwallon da ya ci a wasa na gaba, ya sa Ronaldo ya zama wanda ya fi sauran ‘yan wasan kasar Turai cin kwallaye da yawa a gasannin cin Kofin Duniya a tarihin gasar.
Akwai masoyan Ronaldo da suka rika cika bakin cewa sai gwanin na su ya ci kwallaye tara kafin a kammala gasar, duk kuwa da cewa a wasan Portugal na karshe a rukunin su, ya buga bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma mai tsaron gida ya kama kwallon.
Ci biyu da dayan da Urugay ta yi wa Portugal jiya Asabar, ya karya duk wasu fukafuki da Ronaldo ke faffaka da su idan ya shiga filin kwallo.
Dimbin magoya bayan Messi da Barcelona a duniya sun cika da murna bayan da alkalin wasa ya hura tashi bayan DA Uraguay ta yi galaba a kan Portugal, domin kowa ya san wannan usur da aka hura, an hura wa Ronaldo ne cewa ya kama hanyar garin su, idan ya ga dama ya bi ta hanyar da Messi ya bi ya bar kasar.
Abin haushi, An ci su Ronaldo kwallo ta biyu, a ragar da ya ci Spain kwallaye uku girmis shi kadai.
Yanzu dai Sarkin Mafarautar Ajantina, da abokin adawar sa na Spain, wadanda ake ganin farautar da ake kan ganiyar yi a dajin Rasha duk za su iya komawa gida da naman, giwa, to an samu wani hurtumin tunku ya fatattake su, sun gudu zuwa gida, ba tare da sun kamo ko da janwalagwada, namijin kadangare ba.