Har yanzu dai manyan kasashen da ake sa ran za su ci kofin kwallon kafa ta duniya duk sai waje rod suke yi.
A yammacin Lahadi, kasar Rasha wato mai masaukin baki ta doke kasar Spain a bugun daga kai sai gola.
Kasar Rasha ta jefa kwallaye hudu cikin duka kwallayen da ta buga inda ita kasar spain ta jefa kwallaye biyu ne kawai cikin hudu da ta buga.
Rasha na buga na hudun wasa ya kare.
Yanzu dai suma kasar Spain sun bi sawun kasashen Germany, Argentina, Najeriya, Egypt da sauran kasashen da suka riga sukafice daga wasan.