NYSC: Ba za a tura ‘yan bautar kasa a yankunan da ake zaman dar-dar a Filato ba

0

Hukumar Kula da Masu yi wa Kasa Hidima, NYSC, ta bayyana cewa ba za tura masu aikinn bautar kasa cikin yankunan da ake samun yawaitar tashe-tashen hanuka a jihar Filato ba.

Kodinatan NYSC na jihar Filato, Abdulsalam Alhassan ne ya bayyana haka jiya Litinin a Mangu, jihar Filato.

Alhassan ya bayyana wa wakilin Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa daukar wannan mataki ya zama dole, domin kaucewa barkewar tashin hankali da kuma tabbatar an kiyaye rayukan matasan.

“Mun kuma yanke cewa a za tura su kananan hukumomin da muka tabbatar da cewa ana zaune lafiya da juna a kananan hukumomin.

“Mu na kuma aiki tare da jami’an SSS domin sanin yankunan da ake zaune lafiya da kuma yankin da yaran za a rika isa gare su da gaggawa.”

Ya ce akasarin wadanda a za a tura din, duk za a ajiye su ne a cibiyoyin kananan hukumomi, wato hedikwata, ta yadda duk lokacin da ake son garzaya a wurin su, hakan ba zai iya zama matsala ba.

Ya ci gaba da cewa wadanda aka tura aikin bautar kasa a Bakkos, Barkin Ladi, Mangu da Riyom da kuma wani sashe na Jos ta Kudu, duk an gaggauta ceto su daga yankin zuwa mafaka a a lokacin da aka yi hargitsin cikin watan Yuni. Amma daga baya mun tura su wasu yankuna daban wadanda ba su fama da rikice-rikice a yanzu

Ya kuma ce su na aiki tare da fannonin jami’an tsaro da dama wadanda ke sanar da su halin da masu bautar kasar ke ciki.

Share.

game da Author