Naira 5,000 ake biya na duk kai harin bam daya na na shirya -Inji dan Boko Haram

0

Wani dan Boko Haram mai suna Abubakar Kori, ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram na biyan sa naira dubu biyar a duk harin bam daya da suka kai a cikin Maiduguri.

Kori na daya daga cikin mutane 22 da aka kama bisa zargin hannun su wajen kai hare-haren Boko Haram, ciki har da sace ‘yan matan Chibok.

Kori ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai cewa mai gadi ne a wani gidan mai a unguwar Dalori da ke cikin Maiduguri. Ya ce ya shiga cikin kai hare-hare da dama a cikin watannin da suka shude a cikin Maiduguri.

“Ni aiki na kawai shi ne a ajiye bama-bamai, wanda zai kai harin zai zo ya karba a wuri na, sannan ya wuce ya kai harin.

“A lokuta mabambanta wadanda ke kawo min bama-bamai na ba ni ajiya, daga nan kuma sai a turo wani ya zo ya karba, ya tafi da shi.

“Bayan harin ya yi nasara ne, sai a zo a ba ni naira dubu biyar.

“Masu kawo min ajiyar bama-baman nan suke zaune kusa da mu a cikin Maiduguri. Koda yaushe su kan ce min wani mai suna Ba’Adam ne ke ba su kunshin bama-baman su kawo min ajiya.

“Daga nan sai ma suka gabatar da ni ga Ba’Adam din, wanda shi ne gogarman shirya hare-garen.”

A na sa bangaren, Adam Mustapha da aka fi sani da Ba’Adam, ya amsa laifin kai hare-haren, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan jama’a a Maiduguri.

Ya ce shi ya shirya tada bam a unguwannin Bulunkutu, Baga Road, 33 Artillary Gate, Ofishin Kwastam, Post Office da Garejin Muna duk a cikin Maiduguri.

“Sau biyu a na ba ni naira 200,000 idan an kai hari aka yi nasara.

“Sau da yawa ma sai na rika takura musu kafin su biya ni bayan an kai harin an yi nasara.” Inji Ba’Adam.

Shi ma wani mahauci da ake zargi, mai suna Ibrahim Mala, dan shekara 48, ya ce ya sha taimakawa wajen kai hare-hare, sayar da dabbobin da aka sato da kuma kai wa Boko Haram kayayyakin amfani na yau da kullum.

Mala ya ce shi mazaunin Dalori-Kakere ne, wani kauye da ke wajen Maiduguri, ya ce Boko Haram ne ke kawo masa dabbobin ya rika saida musu, kuma su ne suka ba shi jarin naira dubu 180,000 domin sana’ar sa ta sayar da nama ta tafi daidai.

Ya ce ya samu kudi sosai da wannan harka, har fulotai ya saya da dama, har da na naira 423,000.00.

Da ya ke magana, Abba Kyari, Mataimakin Kwamishina na Jami’an Leken Asirin masu kai farmakin gaggawa, ya ce an kamo wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a jihar Borno da Yobe.

Ya yi kira da jama’a su rika gaggauta kai rahoton duk wani bakon idon da suke tababar harkokin da ya ke yi.

Share.

game da Author