Na fi karfin arcewa da gudu daga Najeriya -Fayose

0

Gwamna mai barin gado na jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana cewa ba zai gudu daga Najeriya zuwa wata kasa ba.

Fayose, wanda aka kayar da jam’iyyar su, PDP a zaben gwamnan jihar Ekiti, ranar Asabar, a yau ya ce idan dokar kariyar da ke kan sa ta kare, lokacin da ya sauka, ba zai tsallake daga Najeriya ba.

Wa’adin gwamnatin sa zai kare ne a cikin watan Oktoba, 2018

“Ba inda zai gudu ya tafi? Ya gudu ya je ina? Me za su iya yi masa? Shin ita EFCC din ce ke hukunta mutum da kan ta ne? Haka kakakin yada labaran Fayose, Lere Olayinka ya furta wa PREMIUM TIMES a Lahadi da dare, inda ya ce ya yi magana da gwamnan dangane da makomar sa yayin da wa’adin sa ya cika, aka cire masa rigar kariya daga jikin sa.

Fayose dai zai mika mulki ne a hannun Fayemi, wanda dama a hannun sa ne ya karba cikin 2014. Zai mika mulkin ranar 16 Ga Oktoba, 2018.

Share.

game da Author