Mutane uku cikin mutane biyar dake dauke da cutar kanjamau ne ke samun magani -UN

0

Majalisar dinkin duniya (UN) ta bayyana cewa mutane uku ne cikin mutane biyar dake dauke da cutar kanjamau ke samun maganin cutar a duniya.

Majalisar ta bayyana haka ne bisa ga rahoton sakamakon binciken da ta gudanar a shekarar 2017.

” Binciken ya kuma nuna cewa mutane miliyan 36.9 ne ke dauke da cutar a duniya wanda daga ciki miliya 15.2 na fama da rashin samun mmagani.

Jami’in majalisar Michel Sidibe ya ce a yanzu haka majalisar na bukatan dala biliyan 7 don dakile yaduwar cutar.

Sidibe yace domin cin ma burin su na kawar da cutar daga nan zuwa 2020 kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya su zage damtse wajen ganin hakan ya faru.

A kasa Najeriya kuwa rahotanni da suka gabata sun nuna cewa gwamnatin Amurka ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 90 da yayi daidai da naira biliyan 32 don yin kididdiga da sanin yawan masu dauke da Kanjamau

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 90 don a san ainihin yawan mutanen dake dauke da cutar Kanjamau a kasar.

Adewole yace bayan Amurka ta bada wannan tallafin za kuma ta aiko da kwararrun ma’aikatan binciken da za su taya kasar gudanar da wannan bincike da za a fara daga watan Yunin 2018.

” Za ayi wannan bincike da kididdiga a dukka jihohin kasar nan sannan zai dauke mu watanni 6 muna yi. Wannan aiki zai taimaka wa gwamnatin Najeriya tsara manufofi da hanyoyin da zai taimaka wajen kawo karshen yaduwar wannan cuta.

Bayan haka Shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau (NACA) Sani Aliyu ya yaba wa wannan tallafi da Najeriya ta samu yana mai cewa hakan zai taimakawa kasar samar da wasu dabarun da zai kawo karshen yaduwar a kasar.

Share.

game da Author