Mutane sama da 22,000 ne suka koma ‘yan gudun hijira a Jihar Filato- Kungiyar Red Cross

0

Jami’ar kungiyar ‘Red Cross (ICRC) Lene Groenkjaer ta bayyana cewa mutane sama da 22,000 ne suka zama ‘yan gudun hijira sanadiyyar tashin tashin din da ake yi fama da shi a jihar Filato.

Groenkjaer ta ce a dalilin haka kungiyar su za ta hada hannu da reshen kungiyar dake jihar Filato a Najeriya domin tallafa wa mutane da rikicin ya shafa.

Ta kuma kara da cewa sanadiyyar wannan rikicin an rasa rayukan mutane da dama, wasu sun sami rauni a jikkunan su sannan da dama sun rasa matsuguni.

Groenkjaer ta ce kungiyar su za ta tallafa wa wadannan mutane da abinci, tufafi, sabulai, gidajen sauro da gina wa sansanonin ban dakuna.

A karshe ta ce kungiyar za ta fi bada karfi ne wurin tallafa wa mata, yara kanana da tsofaffi.
sannan ba za mu yi la’akari ba da addini ko kabilar mutum ba.

Share.

game da Author