Wasu tsararun masu zanga-zangar neman tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun yi dafifi dauke da kwalayen rubuce-rubuce, a hedikwatar jam’iyyar APC da ke kusa da otal din Valencia, a Abuja.
Masu zanga-zangar da suka ce su mambobin APC ne daga jihar Kwara, sun kuma yaba da matakin da uwar jam’iyya ta dauka inda ta rushe shugabancin shugabannin APC na jihar Kwara.
Duk da cewa har yanzu Saraki bai bayyana ficewar sa daga APC ba, ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar ta sa.
Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ce ba za su tsaya sai sun jira har lokacin da Saraki ya fice daga APC a lokacin da ya ga dama ba.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a harabar sakateriyar APC a yau Talata, Tayo Awodiji ya yi kira da a kori Saraki, saboda zagon-kara da ya key i wa jam’iyyar APC.
Yace sun ji dadin rushe shugabannin APC na jihar Kwara da ka yi, ya na mai cewa ai tun tuni ma ya kamata a ce an rushe su.
Awodiji ya ce rushewar zai sa APC ta sake zama daram a jihar Kwara, domin tunkarar zaben 2019.
Masu zanga-zangar sun kuma nemi a sake sabuwar rajistar mambobin APC a jihar Kwara, tare kuma da yi wa dukkan ‘yan majiliasar da suka fice daga APC kiranye.
Awodiyi ya yaba wa sabon shugaban riko na jam’iyyar kuma ya jinjina wa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed.