Mahara sun yi garkuwa da mutane 15 a Zamfara

0

Kakakin Majalisar Jihar Zamfaram Sanusi Rikiji, ya bayyana cewa mahara sun sace mutane 15 a ranar Asabar a cikin Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Rikiji ya bayyana wa manema labarai haka a Gusau, jiya Lahadi, babban birnin jihar.

Ya ci gaba da cewa a gaskiya ya zama dole a sake duba fasalin matsalar tsaro a jihar ta Zamfara.

Ya nanata matsalar da ta faru kwanaki biyu da suka gabata a Zurmi, inda mahara suka mamaye garuruwan hakimai uku, da suka kunshi kauyuka 18 da garuruwa.

“Na fada jiya a Zurmi cewa matsalar tsaro a jihar nan ta na bukatar a sake duba ta gaba daya. Saboda an dade ana wannan kashe-kashe.

“Jami’an tsaro su kara himma da azama sosai wajen karo jami’an tsaro a Zamfara, mu na bukatar sansanoni na dindindin a wadannan yankuna da ake kashe al’ummar mu bagatatan.

“Mu na godiya dangane da shigowar da gwamnatin tarayya ta yi a wannan lamari, domin a yanzu tuni har an tura sojoji a yankin Zurmi.

Ya ce sojoji sun fara maido da zaman lafiya a yankin, kuma su na rokon jam’a su kara hada kai da sojojin domin a samu zaman lafiya.

Haka kuma kakakin ya gode wa Atiku Abubakar dangane da damuwar da ya nuna kan kashe ‘yan jihar Zamfara da mahara ke yi.

Ranar Asabar ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin tura jami’an tsaro 1,000 a jihar Zamfara.

Share.

game da Author