Kwastan sun bayyyana kwace wasu motocin da aka loda wa shinkafar sumogal su 11 a kan hanyar Kaduna zuwa Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa Mataimakin Kwanturola kuma Ekanem Wills ne ya bayyana wa manema labarai haka a Kaduna.
“Mun samu nasarar damke motocin dauke da kimanin buhuna 40 zuwa 45. An samu shinkafar a cikin motoci kirar Golf takwas, J5 guda uku.”
Ya ce ana nan ana bincike yayin da aka damke masu dakon shinkafar.
Tun bayan da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau mulki ta sha alwashin hana shigo da shinkafa.
Sai dai kuma masu karamin karfi na kokawa da jami’an kwastan a kan yadda suke bindige masu dakon shinkafar sumogal ko da buhu biyar ne.