Ku bude idanuwar ku, ku zauna cikin shiri, Sufeto Janar Idris ga Kwamishinonin ‘yan sanda

0

Sufeto Janr din ‘yan sandan kasa Ibrahim Idris ya yi kira ga kwamishinonin ‘Yan sanda da manyan jami’an ‘yan sanda da ke kula da shiyoyin kasar nan cewa su kwana da shiri sannan su zauna cikin shirin ko ta kwana.

Wannan kira da Idris yayi ya biyo bayan bindige wasu ‘yan sanda bakwai da aka yi a unguwar Galadimawa dake babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce bayan haka dakarun ‘yan sanda za su bazu lunguna-lunguna, sako-sako, kwararo-kwararo don zakulo miyagun da ke addabar mutane sannan za ta kuma bi duk inda take ganin maboyar miyagu ne domin taso keyar su da hukunta su.

Share.

game da Author