Killace Fulani wuri daya ba zai magance matsalar tsaro a Arewa ba -Sanata Dansadau

0

Shugaban jam’iyyar NRM, Sanata Sa’idu Dansadau ya bayyyana cewa killace Fulani makiyaya wuri daya da nufi ko da shirin gina musu matsuganar dindindin domin kiwon shanun su, ba zai magance rikici-rikice da matsalar tsaro a Arewacin kasar ba.

Tsohon sanatan daga Jihar Zamfara, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa, NAN a Maiduguri cewa gwamnonin yankin Arewa tilas su tashi tsaye su rika samar da shugabanci nagari, domin magance matsalar tsaro a fadin yankin Arewa.

Ya ce gwamnonin Arewa su yi koyi da gwamnan jihar Lagos, dangane da matakin da ya dauka ya raba jihar da ‘yan dabar OPC.

“Idan za a kwaso dukkan makaman kasar Amurka kakaf, a kwaso sojojin kasar Amurka a kawo nan Najeriya, babu yadda za su iya magance matsalar tsaron Arewa.

“Matsawar shugabanni ba su da adalci, to duk wani shiri ba mai fitar da mu daga kangin rikice-rikice ba ne.

Share.

game da Author