Wata kungiyar bincike dake zaman kanta a New Delhi kasar India ‘Centre for Science and Environment (CSE)’, ta bayyana cewa kashi 90 bisa 100 na gwanjunan motocin da ake shigowa da su kasashen Afrika na cutar da kiwon lafiyar mutanen yankin.
Jami’ar kungiyar ‘Priyanka Chandola’ ta fadi haka a Abuja ranar Talata.
Priyanka ta bayyana cewa sun gano haka ne bayan gudanar da bincike kan illolin da wadannan motoci ke yi wa lafiyar mutane da kuma muhallin su.
” Sakamakon da muka samu ya nuna cewa wadannan motoci na matukar cutar da kiwon lafiyar mutane ta hanayar gurbata iskar da mutane kan shaka.
” Binciken ya kuma nuna cewa a yanzu haka kashi 90 bisa 100 ne ake shigowa da su kasa Najeriya, kashi 85 a Ethiopia, kashi 80 a Kenya sannan duk da haka mutane kalilan ne ke iya siyan mota don hawa na kan su.
A karshe Priyanka ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su kirkiro dokokin da za su hana shigowa da motoci irin haka tare da tsawwala harajin da ake biya wurin shigowa da su.
Discussion about this post