Minista Kemi Adeosun ba ta cancanci karba ko a ba ta satifiket na sahale mata tafiya aikin bautar kasa ba, saboda ikirarin ta na cika shekaru 30. Kai ko da ma da ta nemi a ba ta, to babu yadda za a yi a ba ta din, kamar yadda tsohon shugaban hukumar, Maharazu Tsiga ya bayyana wa PREMIUM TIMES.
A jiya Laraba ne Tsiga, wanda ya fara aiki da NYSC a cikin Janairu, 2009, yay i tattaunawa da PREMIUM TIMES ta wayar tarho, daga gidan sa na Katsina.
Janar Tsiga mai ritaya, ya kara bayar da hasken da ya tabbatar da cewa satifiket din na Kemi na jabu ne.
Ya kara furta maganar da daya daga cikin tsoffin jami’an hukumar da suka yi aiki tare, da shi, Mista Ani ya fada cewa tantance sahihancin satifiket na NYSC ko kuma na bogi abu ne mai sauki.
Ya ce akwai daki mai na’urorin tantance komai, don haka bai ga dalilin da zai sa a bata lokacin wai sai an je wani ko wasu wuraren yin bincike ba, sai fa idan ba a son yin bincken kawai.
Maharazu Tsiga ne ya kamata a ce ya sa mata hannu, amma sai ya kasance satifiket din na dauke da sa hannun Bomai, wanda shi Tsiga din ya gada tun Janairu, 2019.
Satifiket din na Kemi Adeosun na dauke da sa hannun Bomai, kuma ya sa hannun a cikin watan Satumba, 2019, watanni tara cur bayan saukar da daga shugabancin NYSC.
Discussion about this post