Kakakin yada labaran APC ya fice daga jam’iyyar

0

Kakakin Yada Labaran jam’iyyar APC na jihar Benuwai, Agbo Terkula, ya ajiye aikin sa tare da sanarwar ficewa daga jam’iyyar dungurungum.

A cikin wata wasikar ajiye aiki da ya rubuta a jiya Laraba, kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar na jiha, Terkula ya ce kasancewar APC jam’iyya mai mulki a tarayya, bai ga wani abin da ta tsinana wa jihar Benuwai ba, kuma ba ta kare muradin ‘yan jihar a kasa baki daya.

Ya nuna takaicin kashe-kashen da ake yi tsakanin manoman jihar da makiyaya wanda ya ce hakan ya haifar da dimbin mazauna sansanin masu gudun hijira.

Ya ci gaba da cewa wasu munanan kalaman da wasu ‘yan siyasa da ke karkashin gwamnati da ba su yi wa bakin su linzami, ya kara rura wutar kashe-kashen da ke faruwa a kasar nan

Ya ce an tunkare shi cewa ya yi hakuri ya zauna, za a biya masa bukatun sa, amma ya ce shi ba wannan ba ne a gaban sa.

Ya ce tsayawar sa a cikin APC tamkar amincewa da abin da jihar Benuwai da ‘yan jihar ke fuskanta ne.

Share.

game da Author