Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce za ta fitar a ranakun da za ta gudanar da zabukan cike gurabu a jihohin Katsina da Bauchi da Cross River, a mako mai zuwa.
Dukkan zabukan Katsina da na Bauchi dai na cike gurabun Sanatoci biyu ne da suka rasu.
Hukumar ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Kwamishinan ta na Kasa, Mohammed Haruna ya bayyana a jiya Juma’a.
Haruna ya ce a mako mai zuwa kuma hukumar za ta fitar da ranar zaben dan majalisar jiha na mazabar Obudu 1 da ke cikin jihar Cross River.
Haruna ya ce tuni Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dama can ita INEC ta shirya, kawai ta jira samun wasika ne daga Majalisar Dattawa da kuma majalisar jihar Cross River, wanda sai ta samu wasikin ne sannan za ta tabbatar wa duniya cewa kujerun ba su da wakili a kan su, don haka masu nema sai su fito INEC ta shirya musu zabe.
A Katsina akwai kujerar Sanata na Katsina ta Arewa, sai Bauchi kuma Sanata Bauchi ta Kudu.