Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya bayyana cewa ‘yan siyasa sun karkata ne wajen sayen kuri’u, saboda hukumar sa ta toshe duk wata kafa, yadda bai yiwuwa a hada baki da jami’an INEC a yi magudi.
Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi a wurin sauraren rahotannin da kungiyoyin sa-kai wadanda suka halarci zaben gwamnan jihar Ekiti.
Da ya ke jawabi ta bakin Kwamishinar INEC ta Kasa, May Mbu, Farfesa Yakubu ya ce, a yanzu ma’aikatan hukumar na tsoron karbar toshiyar-baki, gudun kada doka ta hau kan sa.
“A yanzu INEC ta toshe duk wata kofar da za a iya yin wuru-wuru, shi ya sa wasu ke sayen kuri’u domin lokaci ya wuce da ake shigewa cikin daki ana rubuta sakamakon zabe.
“Sannan kuma fizgen akwatu a yanzu ba shi da wani amfani, domin kowa ya san duk akwatin da aka sace, to nan take za a soke yawan kuri’un da ke cikin sai.