Ina nan daram a APC, ban waske ba tukunna – Inji Shehu Sani

0

Sanata da ke wakiltan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram dam a Jam’iyyar APC tukunna bai fice ba.

A sako ta musamman da ya aiko wa PREMIUM TIMES, sannan ya saka a shafunan sa na soshiyal midiya sanata Sani yace yana nan a yanzu amma a saurare shi nan ba da dadewa ba.

” Ina so in sanar muku cewa har yanzu ina nan a Jam’iyyar APC ban fice ba tukunna. Sai dai nan ba da dadewa ba zan sanar muku wadda ake ciki.

Shehu Sani ya kara da cewa nan da makonni biyu idan har ma yakai kenan zai bayyana wa mutane shirin sa. Idan ma ficewa yayi, zai fadi inda ya nufa.

A yammacin Juma’a ne kungiyar APC Akida da Sanata Shehu Sani yake mamban kungiyar ce a Kaduna ta sanar da ficewa daga jam’iyyar APC tare da APC Restoration, wanda ake danganta ta da Tijjani Ramalan da sanata Suleiman Hunkuyi.

Tun a makon da ta gabata ne ake ta samun canje-canje da sauye-sauyen yan siyasa inda wasu hasalallun’yan APC suka balle suka kafa sabuwar APC da suka yi wa suna APC na Hakika, wasu kuma sun riga sun bayyana inda suka dosa.

Share.

game da Author