Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya ce hukumar za ta kara daukar ma’aikata har 4,650, tare da samar da motocin zirga-zirgar aikin kara kiyaye rayukan jama’a a kan titinan kasar nan.
Oyeyemi ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa ta musamman da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a Lagos, ranar Lahadi.
An ruwaito shi ya na cewa hukumar ba za ta dauki kowa ba sai wadanda suka fi cancanta, ba ta yi kwasar-karan-mahaukaciya ba.
Ya kuma kara da cewa za a dauki ma’aikatan ne daga nan zuwa karshen wannan shekara, wato a cikin watanni shida na karshen shekara kenan.
“Tunda an rigaya an sa wa kasafin kudi na 2018 hannu, babu wani jinkirin da za mu yi kuma, sai shirin daukar ma’aikata da kuma karo motocin zirga-zirgar ma’aikatan mu domin inganta kiyaye hadurra a kan titinan kasar nan.” Inji Oyeyemi.
“Tuni ma mun fara shirye-shiryen karo motocin da motocin sintiri, motocin garzayawa da wadanda suka yi hadari zuwa asibiti da kuma Babura da su kara inganta ayyukan jami’an mu.”
A karshe ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari kan karin kason kudade da hukumar ta samu a cikin kasafin kudi na 2018.