Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudi Hajji

0

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudi Hajjin bana na 2018 zuwa ranar 25 Ga Yuli.

NAHCON ta bayyana haka a ta bakin jami’ar yada labaran hukumar, Fatima Usara, a cikin wani jawabi da ta fitar a yau Alhamis.

“Duk mai niyyar zuwa da bai kai ga karasa cika kudin sa ba, to zai iya gaggautawa ya biya a cibiyoyin Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar sa ko kuma a hannun ejan ga masu tafiya a jirgin yawo.”

Usara ta ce karin wa’adin rufe karbar kudin ya zama dole, saboda NAHCON ta lura cewa wasu saboda matsaloli na yau da kullum, har yau su na fa fagamniyar neman cikon kudin, kuma su na cike da fargabar kada wannan dama ta zuwa sauke farali ta wuce su.

Kafin wannan kari dai, NAHCON ta yi niyyar rufewa ne a ranar 21 Ga Yuli. Dama kuma tuni hukumar ta bayar da samarwar rufewa, amma daga bisani saboda karancin masu zuwa aikin Hajji a wannan shekara, sai aka rika kara wa’adin.

Share.

game da Author