Sanata Shehu Sani ya ambato wasu hanyoyi dalla-dalla da za a iya bi wajen warware matsala da rashin jituwar da ya kanannade majalisar Tarayya da fadar Shugaban Kasa tun bayan rantsar da wannan gwamnati a 2015.
Sanata Shehu Sani dai na wakiltar Kaduna ta tsakiya ce a majalisar dattawa.
Idan ba a manta ba Sanata Shehu Sani ya amayo habaici a makon da ya gabata cewa suna gab da su fice daga kasar mulkin kama karya inda ya danganta maganar sa da tarihin Annabi Musa da fir’auna na kasar Misra.
Ga hanyoyin da ya ke ganin su ne za a bi a gyara barakar da ke tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa.
1 – A yi maza-maza a daina sarar ‘yan majalisa da gariyon tsana ana muzguna musu sannan ana amfani da karfin gwamnati ana ci musu mutunci.
2 – Shugaban kasa ya tilasta wa jami’an gwamnati su rika girmama majalisar da kuma amsa kiran majlisar idan sun neme su da su bayyana a gaban ta.
3 – Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tilasta wa ministocin sa da manyan jami’an gwamnati da su rika daraja shugaban majalisar dattawa dana wakilai saboda girman ofishin su.
4 – Su kuma a majalisa, ya kamata su gaggauta amincewa da kudurorin da fadar shugaban kasa ta turo majalisar sannan su amince da nade-naden jami’an gwamnati da shugaban kasa ya turo majalisa.
7 – Shugaban Kasa ya hana jami’an gwamnati da ke shirya zanga-zangar suka ga majalisa.
6 – ‘Yan majalisa su daina yin suka ga fadar shugaban kasa, zage-zage da yin habaici.
Sanin kowa cewa tun bayan kaddamar da wannan majalisa ake zaman doya da manja tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa.
Rashin jituwar dai ya samo asaline tun bayan kin amincewa da nadin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da majalisar taki yi.
Sannan har yanzu akwai shugabannin hukumomin gwamnati da majalisar bata amince da su ba.
Kuma kiri-kiri sufeto janar din yan sanda ya ki amsa gayyatar majalisa na ya bayyana a gabanta.
Haka kuma a dan kwanakin baya da suka wuce majalisar ta yi barazanar tsige Shugaban kasa da kan sa.
Duk wadannan dai sune sanata Shehu Sani yake ganin matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa da yasa ba a ga maciji tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa.