Gwamnati ta kama kwalaben Kodin na miliyoyin naira

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa tun da gwamnatin ta kafa dokar hana amfani da sarrafa maganin tari na kodin ta kama kwalaben maganin da ya kai naira miliyan 2.4 a kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Mayu ne gwamnati ta kafa dokar hana shigowa da sarrafa maganin tari da aka hada da sinadarin Kodin.

Akinola yace domin karfara wannan dokar ne ya sa ma’aikatar kiwon lafiya ta kafa kwamitin da za ta tabbatar da cewa sun hana amfani da sarrafa wannan maganin.

” Ma’aikatar kiwon lafiya ta zakulo mutane daga ma’aikatar kiwon lafiya, NAFDAC da kungiyar masana magunguna (PCN) a matsayin mambobin wannan kwamiti.

Share.

game da Author