Majalisar Kolin Shari’ar Musulunci ta koka da yadda Gwamnatin Tarayya ta ki shigar da malaman musulunci cikin shirin karkato da ‘yan Boko Haram kan turba madaidaiciya da ta ke yi.
Mataimakin Sakataren Majalisar mai suna Auwal Abdulaziz ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan bayan kammala wani taron hadin guiwa a Kaduna.
Ya ce tunda dai su ‘yan Boko Haram su na ikirarin cewa musulmai ne, to akwai bukatar shigar da malamai a shirin domin su shawo kan su daga akidar da suka ara suka yafa da sunan Boko Haram.
Taron dai an shirya shi ne tare da hadin guiwa da Cibiyar Kulla Alaka ta Addini da Kyautata Al’adu Mabambanta ta Sarki Abdullah Abdulaziz na Saudi Arabiya.
Auwal ya ce idan aka yi la’akari irin akidun Boko Haram, za a ga cewa akwai bukatar shigar da malamai a sahun farko wajen kokarin dakile musu wancan tunani da akidar ta suka shiga da sunan Boko Haram.
Discussion about this post