Takwas daga cikin mambobin Majalisar Jihar Benuwai 30, sun yi zaman majalisa a yau Litinin, inda suka aika wa Gwamna Samuel Ortom sammacen sanar masa da shirin tsige shi.
Wadannan ‘yan majalisa takwas sun kutsa cikin majalisar tare da goyon bayan ‘yan sanda, kamar yadda Kakakin Gwamnan Jihar, Tahav Agerzua ya bayyana.
“Sun mamaye majalisar, kuma sun aiko wa Gwamna takardar sanarwar shirin tsige shi, duk kuwa da gargadin da kotu ta yi cewa ta haramta su shiga cikin majalisar ko batun tsige gwamnan.
Agerzua yace tsohon gwamnan jihar ne, Sanata George Akume ya dauko ‘yan sanda daga Abuja inda suka yi amfani da ‘yan majalisar wakilai takwas domin tsige gwamna a majalisar da ke da wakilai 30.
Wannan rikici ya faru ne kwanaki kadan bayan Ortom ya fice daga APC, ya koma PDP.
Sannan kuma ya faru ne kwanaki kadan bayan ‘yan majalisa 23 daga PDP sun tsige Kakakin majalisar, Terkimbi Ikyange. Ikenge dai ya nan a cikin APC, duk kuwa da cewa 23 da uku daga cikin 30 din su duk sun koma PDP.