Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya tsige kwamishinoni 9 da masu ba shi shawara biyu daga kan mukaman su.
Wannan sanarwa ta na kunshe ne a cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar, Mohammed Abdullahi ya sa wa hannu kuma ya raba wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a jiya Lahadi a Lafiya.
Abdullahi ya ce an tsige kwamishinonin nan take ba da wani bata lokaci ba.
Sai dai kuma ya ce an cire su ne domin a ba su damar samun lokacin tafiya yin hidimomin siyasar da suke da muradin shiga takatar zaben mukamai daban-daban a zaben 2019.
Wadanda saukewar ta shafa sun hada da Abdullahi Kwarra na Ma’aikatar Muhalli da Raya Karkara, Gabriel Aka’Ka na Harkokin Ruwa, Mary Enwongulu ta Harkokin Mata da kuma Bamaiyi Anagba daga Ma’aikatar Matasa da Wasanni.
Sauran sun hada da Daniel Iya, Kwamishinan Lafiya, Yusuf Usman na Yada Labarai da kuma Sonny Agassi na Kasa da Tsare-tsaren birane.
Akwai Muhammed Yahaya na Maikatar Ayyuka da Gidaje da kuma Tanko Zubair, na Ma’aikatar Cinikayya da Masana’antu da Shakatawa.
Discussion about this post