Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta mallaki takardar shaidar yin bautar kasa ne na jabu, shekaru da yawa bayan da ta kammala jami’a.
Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga wanda duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa hukumar ta ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.

Ga Takardun duka nan: DOCUMENTS: Kemi Adeosun’s fake NYSC certificate and other credentials
Discussion about this post