Rundunar ‘yan sandan Ekiti ta shaida wa manema labari cewa gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya shirga wa dakarun tsaro da ke aiki a jihar da ‘yan sanda karya ce wai a gaban su ake dauke akwatunan zabe.
Daya daga cikin manyan jami’an ‘yan sandan da aka tura wannan jiha domin sa ido a wannan zabe ya karyata wannan zargi na Fayose in da yace jim kadan bayan Fayose ya fadi haka a hira da yayi da manema labarai suka fara bin diddigen abin da ya faru a wajen zaben.
” Mun gano cewa wannan duk zargine irin na ‘yan siyasa amma babu wani abu mai kama da haka da ya faru zuwa yanzu.”
Gwamna Fayose ya zargi jami’an tsaro da yi wa musammam magoya bayan jam’iyya PDP karfa-karfa da taimakawa jam’iyyar adawa a yi wa PDP murdiyya.
Bimu Kai tsaye a nan: