FASHIN OFFA: Ba mu hakura da binciken Saraki ba – Moshood Jimoh

0

‘Yan sandan Najeriya sun ci gaba da binciken Sanata Bukola Saraki jiya Alhamis, kamar yadda ya gayyace su zuwa ofishin sa ya ce su je can su bincike shi.

Kakakin Yada Labaran su Jimoh Moshood ya bayyana cewa labarin da PREMIUM TIMES ta buga wanda ya nuna cewa Ministan Shari’a Abubakar Malami ya wanke Saraki daga laifi, ba wai ana nufin ba za a ci gaba da bincike ba ne.

Moshood ya ce za a ci gaba da bincike, domin wasu cikin wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a fashin, sun makala sunan Saraki a fashin wanda aka yi a garin Offa, cikin watan Afrilu.

Moshood ya yi wannan jawabi ne sa’o’i kadan bayan da PREMIUM TIMES ta buga labarin wasikar da Malami ya rubuta wa Sufeto Janar cewa ba su da wata shaidar da ta nuna Saraki da gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kwara na da hannu a fashin.

Malami ya nuna cewa ‘yan sanda sun yi azarbabin makala wa su Saraki laifin fashi ba tare da wasu kwararan bincike ko shaidu ba. Sai dai kuma ya shawarce su da cewa za su iya fadada binciken su idan ba su gamsu da iyar binciken da suka yi ba.

Wannan wasika dai Babban Daraktan Gabatar da Kara, Mohammed Umar ne ya sa mata hannu a madadin Minista Malami, kuma Jimoh ya ce shawara ce ya ba ‘yan sanda ba wanke su Saraki ya yi ba.

Share.

game da Author