Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi cewa gwamnatin tarayya za ta kara wa fannin kiwon lafiya kason kudin da take samu a kasafin kudi na 2018.
Buhari ya fadi haka ne a lokacin da sabin shugabanin kungiyar likitoci na kasa (NMA) suka ziyarce shi a fadan shugaban kasa.
Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta aiyukkan fannin domin samar wa mutane ingantaciyyar kiwon lafiyar da ya kamata kasan.
Sanin kowa ne cewa fannin kiwon lafiyar Najeriya ta gurgunce sanadiyyar rashin ware mata isassun kudade da gwamnatin Najeria bata yi.
A dalilin wannan matsala talakawa sun gwammace su nemi maganin cutar dake damun su daga magungunanta hanyar magungunar gargajiya sannan attajirai kuwa su kan fita ne zuwa kasashen waje.
A yanzu dai ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta amince ta ware kaso mai tsoka domin bunkasa aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiyar dake kasar.
” A shekarun baya mun dauki matakin bunkasa asibitocin koyarwa a kasar nan domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya amma sai muka gano cewa talaka da ke zaune a kauye baya iya zuwa wadannan asibitocin.
” A dalilin haka muka amince mu bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar kara musu kason kudaden da suke samu daga kashi 18 zuwa 64 bisa 100 domin inganta kiwon lafiya a kasar.
A karshe Adewole yace suna sa ran cewa wannan dabaran za ta taimaka wa gwamnati wurin shawo kan matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar ke fama da su.