Fadar Shugaban Kasa za ta buga sunayen mutane 200 da masu guntun kashi a baya

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ta na shirye-shiryen buga sunayen wasu da ake zargin sun waruri kudade, har mutum 200.

Mutanen ana zargin sun azurta kan su ta hanyar kwasar su dadaden suka mallaki kadarori.

Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara na Musamman a kan Gurfanar da Mazambata Kotu, Okoi Obono-Obla, shi ya fadi haka a lokacin da yake jawabi wurin taron kungiyar ANEEJ a Abuja.

Jaridar Daily Trust ruwaito jiya Alhamis cewa, Obla bai yi karin hasken ko za a gurfanar da su a gaban kotu bayan buga sunayen ko a’a ba.

Kokarin jin karin bayani daga bakin Obla da PREMIUM TIMES ta yi, ya ci tura.

Rahoton ya nuna cewa za a umarci masu kadarorin da su fito su kawo hujjojin yadda aka yi suka mallake su, ko kuma idan ba za a su iya yin gamsasshen bayani ba, to za a maida dukiyar a baitilmalin kasa.

Rahoton ya kara da cewa tuni an gama tsaya fayyace wadanda suka mallaki manyan kadarori a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Share.

game da Author